MEI ZAKI JI BAYAN HAMFANI DA KWAYOYIN ZUBARDA CIKI?

Murdan Ciki da zubar jinni sune manyan illolin.wadannan alamomim sunada muhimmanci saboda zasu nuna ko maganin yana aiki .Amma yaya yanayin Murdan ciki da zubar jinin da zaki samun yake?

  • Wasu Mata murdan ciki ya tsanani fiye da murdan ciki al’ada( In ke maisamu murdan ciki aláda ne)
  • Wasu mata zubar jinni yakan tsananta fiye da jinin al’ada.Har zaki iya samun gudajin jini kamar girman kwan kaza kadan daga cikin awoyin farko da kika sha misoprostol.
  • Wasu Mata murdan ciki da zubar jinni kadan ne kamar sunayin al’adan su.

MUNA SON KI KASANCE DA SHIRI !

  • Kar kisamu damuwa in kinsamu zubar jinni mai yawa da murdan ciki fiye da al’adar ki.
  • In har kinsamu murder ciki mai tsanani ibuprofen zai tamaka sosai don samun saukin murdar ciki.Zaki iya sayan ibuprofen 200mg wurin sayan magani koda Likita bai rubutaba awosu kasashen.Kwayan uku zuwa hudu 2-3 (200mg) kowace awa shida zuwa takwas zai sa kisamu sauki.

AKULA!

Lokacin da ki ke da ciki,alamomin na sama ba abun damuwa bane.Amma akula alamomina kasa za su iye jefa ki cikin matsala.

  • Zubar jinni mai tsanani:In auduga biyu manya sun cika cikin awa biyu alokaci daya bayen kina tunanen ciki ya fita.
    blood-pad hausa_v1To wannan jinin ya tsananta.Anemi taimakon likita.
  • Jikewar audugan yana nufi babbar auduga tacika da jinni gaba da baya,gefe da gefe da kuma cikinta gabadaya.
  • Murdan ciki mai tsanani:In kin sami tsanani wanda aka kasa samun sauki duk da kinsha ibuprofen,to ki naimi taimakon likita.Wannan irin murdar ciki mai tsanani zai iya sa ki samu matsala dangane da ciki.Murdar Ciki da aka kasa samu sauki tare da amfani da ibuprofen zai iya zama alamar matsala.Muna bada shawara duk mace mai ciki da ke famar da murdar ciki ta nemi taimakon Likita.