Bayani zubar da ciki tare da yardar likita

Zubar da ciki na likitanci, wanda kuma aka sani da zubar da ciki na likitanci, yana faruwa yayinda aka yi amfani da ƙwayoyin magani domin kawo ƙarshen ciki. Za a iya amfani da ƙwayar maganin zubar da ciki na likitanci ta mifepristone tare da misoprostol, ko misoprostol kawai. Za a iya amfani da ƙwayoyin maganin kodai ta sakawa a farji ko kuma a saka su a ƙarƙashin harshe. To amma, muna ba da shawarar amfani da su ta hanyar sakawa a ƙarƙashin harshe domin kaucewa ganowa. Ƙungiyar Lafiya ta Duniya ta lissafa zubar da ciki na likitanci a matsayin wata hanya ta kula-da-kai wanda ba lallai sai ta buƙaci sa-ido ba daga wurin ƙwararren masanin lafiya. Wannan yana nufin zai iya kasancewa wanda mutum zai iya yi da kan sa daga cikin gidansa cikin jin daɗi. Tsarin HowToUseAbortionPill an nufeshi ne domin cikin da ya kai har makonni 13.

About Medical Abortion
How it Works Abortion Pills

Yadda Maganin Zubar da Ciki Yake Aiki

Mifepristone yana dakatar da ci gaban girman ciki, kuma yana taimakawa wurin buɗe bakin mahaifa (mashiga zuwa cikin mahaifa). Misoprostol yana sa wa mahaifa ta tsuke, wanda daga ƙarshe zai turo cikin waje.

Da zaran misoprostol ya bi cikin jiki, takurewar fatar ciki da kuma zubar jini za su fara. Yawaici wannan yana farawa a cikin awanni 1 zuwa 2 na jerin farko na ƙwayoyin. Yawaici zubar da cikin yana faruwa cikin awanni 24 da shan ƙwayoyin maganin misoprostol na ƙarshe. Wani lokacin, yana faruwa kafin wannan.

An Samu Damuwa Bayan Shan Maganin Zubar da Ciki?

A ƙasa ga wasu hanyoyi kaɗan na yadda za a gane idan an sami nasarar zubar da ciki:

  • Za ki gane tsokar cikin yayinda yake fita. Yana kama da baƙin gudan jini mai launi a cikin tarkacen, ko kuma wata ƙaramar jaka wadda wata farar tsoka maras kauri ta lulluɓe. Ya danganta da tsufan cikin, zai iya kasancewa ƙarami ƙasa da farcen ɗan yatsa, ko kuma har zuwa girman babban ɗan yatsa.
  • Zubar jini lokacin aiwatar da zubar da cikin wani lokaci yana kama da jinin al’ada, ko kuma ya iya kasancewa fiye da haka.
  • Alamomin cikinki zai inganta. Abubuwa kamar ciwon nono, tashin zuciya, da gajiya za su fara domin samun sauƙi.

Nassoshi:

HowToUseAbortionPill.org na da alaka da kungiya mai zaman kanta wanda ke da rajista a kasar Amurka 501c(3)
HowToUseAbortionPill.org na bada bayani don wayarwa ne kadai, kuma bata da alaka da wani kungiyar lafiya

    Ɗaukar nauyi daga Women First Digital