Mu Su Wanene Kuma Manene Matuƙar Wannan Manufa:

HowToUseAbortionPill (ƙungiyar ko Mu) ƙungiyar ba ta neman riba ba ce wadda ke ba da wani tsari na zamani dake da yanar-gizo da kuma fasahohin da suka dace domin haɗa mutane a faɗin duniya domin daidaitawa da kuma tsara bayanai a kan hanya mafi lafiya ta zubar da ciki da ƙwayoyin magani, ba su damar samun hanya mafi lafiya ta zubar da ciki a kan ƙa’idojinsa (tsari). Tsarin yana tattara bayanan mutane da aka gano (PII) dangane da masu amfani na su, wanda ya haɗa da jami’ai na Ƙungiyar, masu aikace-aikace masu zaman kan su, da kuma masu neman aiki (Masu Amfani). Wannan Manufar Tsaro ta yi cikakken bayani game da nau’ikan PII da muka tattara da kuma haƙƙoƙin Masu Amfani dangane da PII na su. Yayinda muke sarrafa yawaicin ɓangarori na Tsarin, Wasu Masu Samarwa na Waje ne ke samar da su domin haɓaka ingancinsa.
Wannan Manufar Sirrin an kafa ta ne domin kare sirrin Masu Amfani.

Canje-canje Ga Wannan Manufa Da Kuma Ƙarin Sanarwa Ta Sirri

Mu muke da damar yin gyara ga wannan Manufar Sirri a nan gaba. Ba za mu sanar da masu amfani wasu ƙananan canje-canje waɗanda ba za su shafi sirrinsu sosai ba – kamar samar da inganta tsaron sirri, gyara kurakurai na rubutu, ko kuma ƙara wani bayani. Domin kowane irin muhimmin canji, za mu sanar da masu amfani ta hanyar saƙon imel. Idan babu ingantaccen adireshin imel daga mai amfani, ba za mu iya sanar da su kowaɗanne canje-canjen Manufofi ba. Za a iya sabunta wannan Manufar Sirri ko ƙara wani bayani daga gare mu ta hanyar samar da sabon ɗab’i ko kuma ƙarin bayanai na sirri waɗanda suka dace da hulɗoɗinmu da ke. Ana iya haɗa waɗannan bayanai a cikin wannan Manufa, aikawa a dandalin yanar-gizo na Ƙungyarmu, da/ko a samar maka da ita daban.

Kafofi Na Dandalolin Wasu Daban

Wannan Manufar Sirri ba ta shafi wasu dandaloli na wasu daban ba wanda ke iya haɗawa da ko kuma ake samu daga Tsarin. Ba mu ke da alhakin abinda ke ciki ba, fasaloli, aiki, ko kuma aiwatar da manufa na irin waɗannan dandaloli ko aikace-aikace. Bayanan da aka tattara da kuma amfani da dandalolin da aka haɗa na wasu daban suna samun kulawa ne daga sanarwar sirri na wannan dandamalin da abin ya shafa, bayani, ko manufa. Muna ƙarfafa maka gwiwa da ka karanta su.

Fayyatattun Bayanai Na Ƙashin-kai Da Aka Tattara:

A wannan Manufar Sirri, dukkan fayyatattun bayanai na ƙashin-kai ana kiransu a jumlace “PII.” Muna tattara PII masu dama daga kuma dangane da Masu Amfani, ya danganta da matsayin. Sabodahaka, PII na iya haɗawa da:

  • Suna.
  • Adireshin Imel.
  • Lambar waya.
  • Adireshin IP, mai bayar da sabis na intanet, nau’in burauza, da kuma yare.
  • Wurin zama.
  • Lokacin Yanki.
  • Yarukan da aka yi amfani da su.
  • Shekara, jinsi, hotuna na ƙashin-kai, da sauran bayanai da Masu Amfani suka bayar.
  • Bayanan da Masu Amfani suke bayar dangane da lafiyarsu, matsalolin haihuwa/ciki, dalilan hulɗa da Tsarin, da kuma iyawarsu ta samun dama da kuma biya domin sabis-sabis na kula da haihuwa.
  • Matsayin aikin yi da kuma bayanin mai ɗaukar aiki.
  • Takardar shaida da kimantawa da kowane ɓangare na Tsarin.

Tattara Bayananka Na Ƙashin-kai:

Muna neman izini kafin tattara PII. Ta hanyar hulɗa da Tsarin, Masu amfani sun amince da (1) sharuɗɗan wannan Manufar Sirri sannan (2) ga tattarawarmu, amfani, da tsare bayanan da suka bayar sannan kuma Tsarin yana tattarawa daga fasahar da aka yi amfani da ita.
Abinda ake nufi shine, duk lokacin da Mai Amfani ya yi hulɗa da Tsarin, zai tattara PII kai tsaye daga fasahar da Mai Amfani yake amfani da ita kuma zai tattara kowane PII wanda Mai Amfani ya bayar lokacin dukkan wata hulɗa da Tsarin.
Hnyoyin Tattara Bayanai Na Ƙashin-kai:

  • Godunmowa ta sa-kai daga Masu Amfani;
  • Hulɗar Masu Amfani da Tsarin, wanda ya haɗa da Wasu Daban Masu Bayar da Sabis.
  • Tattaunawa da Masu Amfani.

Muna ci gaba da neman hanyoyin tattara PII masu inganci da tsaro, kuma za mu sabunta wannan Manufar Sirri domin nuna waɗannan sabbin hanyoyi.

Yaya Muke Amfani Da Bayanai Na Ƙashin-kai Na Ka:

Muna amfani da PII da muka tattara da/ko sarrafa ta waɗannan hanyoyi:

  • Domin hulɗa da mu a matsayinki na Mai Amfani wanda ya haɗa da amman bai taƙaita ba ga bayanan da suka dace da kuma taimakawa dake da dangantaka da zaɓuɓɓukanki na haihuwa.
  • Nazarin dukkan PII ta yadda za mu inganta sabis-sabis, kayayyaki, da kuma kimar abinda muke isarwa da/ko sadar da irin waɗannan ingantawa da kuma bayanai masu alaƙa ga Masu Amfani da Wasu.
  • Aiwatar da wasu aikace-aikace na gudanarwa domin Tsarin da/ko lokacin aukuwar aiki da kuma ayyukan Ƙungiyar.
  • Aiwatar da bincike domin da/ko daga Ƙungiyar.
  • Domin wasu kwasa-kwasai na koyo a kan yanar-gizo da muke samarwa haɗin-gwiwa da wasu ƙungiyoyi, muna ba wa sauran ƙungiyoyin wasu PII da muka tattara game da mambobinsu waɗanda suka shiga cikin irin waɗannan kwasa-kwasai na yanar-gizo.
    Yinƙurin tattara kuɗaɗe, wanda ya haɗa da samar da taƙaitaccen bayani na PII ga wasu waɗanda suke bayarwa ko za su iya bayar da kuɗaɗe ga Ƙungiyar.
  • Bayar da PII ga jami’an tsaro, wasu wakilai na gwamnati da hukumomi, ko wasu daban kamar yadda dokar da ta dace ta tanada, umarnin kotu, tilasci daga kotu, ko wata aiwatarwa ta shari’a da aka bayar ga Ƙungiyar.

Za mu ɗauki matakai da suka dace kuma bisa doka domin kaucewa tilasta mana bayyana PII na ki ga kowane sashi na gwamnati ko wasu daban da suka nema samun dama gare shi. To amma,, akwai wasu lokutan da sashin gwamnati da/ko wasu daban suke da dama bisa doka su tilastawa wani sashi kamar Ƙungiyarmu su bayyana PII; sannan, a irin wannan yanayi, ya zama wajibi ga Ƙungiyarmu ta yi biyayya.
Game da PII da aka tattara da/ko Masu Bayar da Sabis na wasu daban suka adana da suka shiga cikin Tsarin, ba za mu iya sarrafa amfaninsu ba da/ko adana kowane irin wannan PII.
Kamar yadda aka bayyana a sashin wannan Manufar Sirri mai taken “DAMARKA A KAN BAYANANKA NA ƘASHIN-KAI”, za ki iya yin tasiri a kan abinda muke yi da PII na ki kamar yadda aka fayyace a wancan sashin.

Damarki a Kan Bayananki Na Ƙashin-kai:

Damammakin Mai Amfani dangane da PII na su ya haɗa da:

  • Samun dama da kuma karɓar kwafi-kwafi na PII na su.
  • Fahimtar yadda aka samu PII na ku kuma aka yi amfani da su.
  • Gyara ko goge PII na su.
  • Gyara yadda za mu yi amfani da PII na su.

Domin aiwatar da kowace na waɗannan damammaki, ya zama wajibi Masu Amfani su bayar da adireshin imel wanda yake sahihi kuma wanda aka tantance sannan su bi umarnin da aka zayyana a ƙasa a sashin wannan Manufar Sirri wanda aka yi wa take “YADDA ZAKA TUNTUƁEMU DA NEMA, SHARHOHI, DA TAMBAYOYI”. Idan Mai amfani bai bayar da sahihin imel, kuma wanda aka tantance ba, ba za mu iya tuntuɓarsu ba; sannan wannan zai hana (1) mu daga sanar da su dangane da canje-canje ga wannan manufar da/ko matsaloli dake da dangantaka da PII na su (2) kuma mu daga tantance gano su ta yadda za mu bari su yi amfani da damarsu domin su samu, gyarawa, sarrafawa da kuma goge PII na su.

Manufar Ƙungiya Da Ta Shafi Sirrin Yara Da Kuma Aiwatarwa:

Ba ma tattara bayanai na yara da suke ƙasa da shekaru 13 muna sane. Tunda Tsarinmu ba ya nufin yara, ba ma tantance masu amfani bisa shekarunsu ta amfani da dandalin yanar-gizonmu da kuma sabis-sabis na mu. Wannan yana nufin cewa za mu iya tattara wasu PII ba tare da sani ko nufi ba daga yara ƙanana waɗanda suke amfani da Tsarinmu. Idan Masu Amfani suka bayar da PII dangane da mutanen dake ƙasa da shekaru 13, Ƙungiyar za ta ɗauki wannan PII kamar yadda wannan Manufar Sirri ta tanada. Idan muna sane muka yi hulɗa da wani mutum dake ƙasa da shekaru 13, za mu umarci wannan mutumin da cewa yana buƙatar amincewar iyaye domin hulɗa da Tsarin.

Manufofin Riƙewa Da Aiwatar Da Tsaron Bayani:

Domin kare PII na ki, mun ɗauki waɗannan matakai:

  • Ilmantarwa dangane da wannan Manufa: Muna kan ilmartar da jami’anmu, masu alaƙa da mu, da kuma wasu daban Masu Bayar da Sabis dangane da cikakken bayanin wannan Manufar Sirri, muna jaddada muhimmin matsayi na kare samun dama maras izini ko kuma amfani da PII dake ƙarƙashin kulawarsu.
  • Inganta tsaro: Ci gaban da muke yi na inganta tsaron PII yana nunawa a cikin yinƙurinmu na yanzu. Tuni mun saka wasu hanyoyin tsaro masu yawa dake da zimmar daƙile samun dama maras izini da kuma amfani ba yadda ya dace ba da PII. Bayan kammala haɓaka yinƙurinmu na tsaro, za mu bayar da taƙaitaccen bayani na waɗannan matakai a wannan Manufar Sirri. Saki jikinki ki tuntuɓemu domin kowane irin bayani.
  • Manufar Tsare Bayani: Bisa yadda aka saba, yadda muke yi shi ne goge dukkan PII shekara guda bayan an same shi. To amma, sakamakon sarƙaƙiyar Tsarinmu, ba kodayasushe hakan yake samuwa ba. Yana da muhimmnaci a lura cewa wannan manufar tsarewar ba ya haɗawa da PII wanda Masu Samar da Sabis na wani daban ya tattara ko ya ajiye.
  • Manufar ɓoye bayani: Amincewa da sarƙaƙiyar ɓoye PII da aka tattara, muna kan gyara Tsarinmu domin tabbatar da kammala ɓoyewa na PII. A halin yanzu, ba a riga an kammala aiwatar da wannan mataki ba a kan dukkan PII. Bugu da ƙari, wannan ɓoyewa bai haɗa da PII dake tsaron Masu Bayar da Sabis na wasu daban ba.
  • Masu Bayar da Sabis Wasu Daban: Dangane da Masu Bayar da Sabis wasu daban, ba mu riga mun gudanar da wata tantacewa mai zaman kanta ba na matakan tsaron da suka yi iƙirari. Wannan tantacewa mai zaman kanta tana da tsada sosai da kuma cin lokaci ga kowa
  • kamar Ƙungiyarmu; kuma yawaicin masu samar da sabis na wasu daban ba za su bari a aiwatar da wannan tantacewa ba. για μια οντότητα όπως ο Οργανισμός μας- και οι περισσότεροι πάροχοι υπηρεσιών τρίτων δεν επιτρέπουν τη διενέργεια αυτών των αξιολογήσεων.

Bayyanawa Ta “KADA ABIBIYA”:

Ba ma bibiyar mutane a faɗin dandalin yanar-gizo na wasu daban domin samar da talla da aka nufi wasu. Sabodahaka, ba ma bayar da amsa ga siginoni na Kada A Bibiya (DNT).

Yadda Za a Tuntuɓemu Domin Nema, Sharhohi Da Tambayoyi:

Domin nema, sharhohi, ko tambayoyi, aiko mana da imel a info@howtouseabortionpill.org. Muna tantance ganowa ta amfani da imel na kan fayil kafin tattauna PII.
Kamar yadda aka ambata a sama, idan wani Mai Amfani bai bayar da sahihi kuma adireshin imel da aka tantance ba lokacin da yake hulɗa da mu kuma ya ba mu PII, ba za mu iya tantance su ba daga baya; wannan kuma zai hana mu daga barin kowa ya yi amfani da damammakinsa dake da dangantaka da PII dake mallakinmu.

Sabuntawar Ƙarshe:

An sabunta wannan Manufar Sirri a 1 ga watan Janairu, 2025. Za mu sabunta wannan Manufar Sirri aƙalla sau daya a kowanne watanni 12.