Gudanar da kai na zubar da ciki

An tsara wannan darasin akan layi don duk wanda ke neman ƙarin koyo game da zubar da ciki mai sarrafa kansa, ko zubar da ciki a gida. Tare da bayanan da za ku koya a cikin wannan karatun, zaku iya taimakawa don tabbatar da cewa zubar da ciki tare da kwayoyi suna da aminci, isa, da amintattu. An samar da wannan kwas ɗin cikin haɗin gwiwa tsakanin Médecins Sans Frontières da www.HowToUseAbortionPill.org

Darasi na 1. Ina da ciki?:

Kina son ki samu tabbaci akan cikinki? Nemo wannan bidiyon domin samun bayanin da yake da alaƙa da tabbatar da ciki

Ciki, Mai Ciki

Ciki duka biyun wanda aka shiryawa da wanda ba a shirya masa ba – abu ne da aka saba da shi sosai.

A duk faɗin duniya, sama da kashi 40% na juna biyu a duk duniya ba a shirya mu su ba.

Idan baki so ɗaukar ciki ba amma kika yi tunani ko kin yi, ba ke kaɗai bace.

A cikin wannan bidiyon, za mu yi tattauna a kan yadda zaki tabbatar da daukar ciki.

Da farko dai, abu ne mai muhimmanci ki sani cewa ciki yana samuwa ne bayan saduwa a yayin da maniyi ya harbu daga azzakari zuwa cikin farji.

Dabarun hana ɗaukar ciki na taimakawa wajen hana ɗaukar ciki a yayin saduwa, amma akwai ƴar ƙaramar dama na yiwuwar ɗaukar cikin.

Alama mafi sauri kuma abar dogaro ga ɗaukar ciki shine ɓatan wata.

Idan aka sadu da ke sannan kika fahimci zubar jininki ya makara, ta iya yiwuwa kin ɗauki ciki.

Sauran sanannun alamun ɗaukar ciki sun haɗar da amai, ciwon kai, kasala, buɗewa, zafin nono.

Idan kina da ɗaya daga cikin waɗannan alamun, ƙari akan ɓatan watan, akwai ƙwaƙƙwaran zato cewa kina da ciki.

Idan kina tunanin kin ɗauki ciki, zaki iya gwadawa ta hanyar gwajin fitsari.

Kayan gwajin ɗaukar ciki ana saida su sosai a ɗakunan saida magunguna da shagunan ƙawa, ko kuma ki je cibiyar kula da lafiya domin ki samo.

Ba dole bane ki fara gwajin ciki kafin ki zubar-da-ciki da kwayaoyi.

Idan kin samu alamu da yanayi na ɗaukar ciki, ko kuma in gwajin ya tabbatar da cikin, amma bakya son samun cikin, zaki iya kawar da cikin.

Zubar-da-ciki ka iya samuwa ko dai ta kwayoyi ko kuma ta hanyar tiyata.

Bibiyi wannan bidiyoyin tunda mun samar da gaskiya, bayanan da ke da tabbaci sannan an amsa tambayoyin da aka fi yi a kan zubar-da-ciki da kwayoyi kafin sati na 13.

A cikin bidiyonmu na gaba, mun amsa tambaya, “Yaya daɗewar cikina?”